2019: Kabilar Igbo sunce baza su zabi Atiku ba
- Shugabannin kabilar Igbo sun karyata jita - jitar da ake yadawa na cewar sun tsayar da Atiku a matsayin dan takarar su
- Sunce hakan ya sabawa al'adun su, kuma abin kunya ne yin hakan ga kabilar su
A jiya ne shugabannin Kabilar Igbo dake jihar Bayelsa suka karyata jita - jitar da ake yadawa na cewar sun tsayar da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasar su a shekarar 2019.
DUBA WANNAN: Najeriya zata kai karar Lafari wajen FIFA
Kabilar sunce hakan ya sabawa dokoki da kuma al'adun kabilar su, sun kuma bayyana hakan a matsayin abin kunya ga kabilat tasu.
Shugaban kabilar na jihar Bayelsa, Cif Nkem Mark, shine ya bayyana hakan a lokacin da suke ganawa da sauran shugabannin kabilar na karamar hukumar Ogbia, wanda aka gabatar a kauyen Imiringi dake jihar ta Bayelsa.
Ya ce daga yaya zasu tsayara da Atiku bayan har yanzu jam'iyyar PDP bata tsayar da dan takarar ta ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng