Nigerian news All categories All tags
Zanyi kamun kazar kuku ga 'yan siyasar dake daukar nauyin kashe-kashe

Zanyi kamun kazar kuku ga 'yan siyasar dake daukar nauyin kashe-kashe

- Ana gab da shiga zabuka a kasar nan, wasu na ganin ana amfani da yaki da rashawa don gallazawa masu adawa

- Shugaba Buhari ya shafe tenuwarsa kaf kan yaki da rashawa

- Da yawan 'yan siyasa sun zille saboda sun biiya cin hanci ga hukumomi

Zanyi kamun kazar kuku ga 'yan siyasar dake daukar nauyin kashe-kashe

Zanyi kamun kazar kuku ga 'yan siyasar dake daukar nauyin kashe-kashe

A jawabinsa na taya sojojin kasar nan murna a ranar Army Day a dazu a Monguno, ta jihar Borno, shugaba Buhari ya ce, gwamnatinsa zata dauki babban mataki kan 'yan siyasar da duk aka samu da hannu cikin kashe-kash da ake yi.

Wannan na nufin gwamnatin tana zargin cewa akwai wata makarkashiya da ake yi wa gwamnatin da jama'ar kasar nan, domin cimma burikan siyasa.

An dai ta yamadidi da cewa wai ai shugaban, yana daukar naauyin Fulani makiyaya ne domin ya kashe kirista wai don ya daukaka addinin Islama ta hanyar jihadi, batu da ya karyata.

DUBA WANNAN: Anyi mare-mare a gidan gwamnati

Wasu masu adawa da gwamnati dai kanyi gugar zana kuma su soki shugaban da sakaci ko goya wa makiyaya baya, wadanda ke dauk daidai a jihohin tsakiyar Najeriya.

Watakil dai, in batun da gaske ne akwai siyasa a ciki, wasu ke son shugaban ya rasa kuri'un jihohin, musamman Pilato, Taraba, Binuwai da Kwara, wadanda ta'addancin yafi shafa.

Ana ma zargin shugaban majalisar dattijai da abokansa irin su Dino Melaye, da hannu wajen yadazub da jinane, zargi da har yanzu ba'a kai ga gama bincikarsa ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel