Shedanun mutane ne kadai ke ikirarin cewa ni nake sa ayi kashe-kashe - Buhari

Shedanun mutane ne kadai ke ikirarin cewa ni nake sa ayi kashe-kashe - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari yace ikirarin da wasu mutane keyi na cewa saboda shi bafulatani ne saboda haka baya damuwa da kashe-kashen da ake ikirarin makiyaya nayi a wasu sassan kasar nan tsabar rashin adalci ne a gareshi.

Shugaban kasar ya yi mamakin yadda mutane masu cikaken hankali za suyi tunanin a matsayinsa na shugaba wanda mutane da dama suka jefa masa kuri'a zai bari wani abu mara kyau ya faru dasu da gangan.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun samu gawar 'yan ta'addan Zamfara 41 da aka kashe

Buhari ya yi wannan jawabin ne yayin da yake karbar bakuncin mambobin kungiyar mabiya addinin kirista ta Najeriya (CAN) daga jihohi 19 da suka kai masa ziyara a fadar gwamnati na Aso Villa dake Abuja.

Shedanun mutane ne kawai zasu ce ina goyon bayan kashe-kashen - Buhari
Shedanun mutane ne kawai zasu ce ina goyon bayan kashe-kashen - Buhari

Shugaba Buhari ya ce ba'ayi masa adalci ko kadan ba idan aka ce baya tabuka komai don ganin ya kawo karshen kashe-kashen.

Kalamansa, "Saboda siyasa wasu mutane suna ikirarin cewa gwamnati bata daukan mataki don kawo karshen kashe-kashe kuma suna cewa kasancewa ta bafulatani ina goyon bayan wannan kashe-kashe ba komai bane illa alamar irin zaluncin da dan adan ke iya aikatawa.

"Bugu da kari dukkan gwamnatocin da suka gabata sunyi fama da matsalar kashe-kashe a wadanan wuraren saboda haka rikice-rikicen sun dade suna faruwa.

"Idan ba'a manta ba a shekarar 2001, an kashe dubban mutane a Filato hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta dakatar da gwamnan jihar kuma ta saka dokar da baci a jihar. Ba'ayi mana adalci ba idan aka ce gwamnatin mu bata tabuka komai a kan rikicin."

Shugaban kasan ya bayyana cewa gwamnati ta aike da karin sojoji na musamman daga hedkwatan tsaro na kasa kuma a kalla akwai wasu sojojin samar da zaman lafiya kashi uku a jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164