Hatsarin tankar dakon man fetur 5 mafi muni da suka faru a 2018
'Yan Najeriya musamman mazauna jihar Legas zasu dade basu manta da ranar 28 ga watan Yunin shekarar 2018 ba saboda a ranar ne a kalla mutane 12 suka rasa rayyukansu kuma sama da motocci 50 suka kone kurmus sakamakon wata hatsarin tankar dakon man fetur da ya haifar da gobara.
Kamar yadda Kakakin hukumar bayar da agaji na Legas, Kehinde Adebayo ya bayyana, motar dakon man tana dauke da Lita 33,000 na man fetur ne kuma ta fashe ta kama da wuta inda daga nan ne motoccin dake gefenta suma suka kama da wutan.
Hakan yasa Legit.ng ta yi waiwaye ta kawo muku hadduran tankan dakon mai fetur biyar da suka faru a shekarar 2018.
DUBA WANNAN: Alhaki: Bayan fashin mota, ya yi hadari ya mutu a ciki garin tserewa
1) Hatsarin tankan man fetur na titin Isheri a Legas.
Hatsarin ya faru ne a ranar Juma'a 19 ga watan Janairu a titin Isheri zuwa Lasu sai dai Allaha ya takaita babu wanda ya rasu sakamakon hatsarin.
2) Hatsarin tankan man fetur na titin Legas - Ibadan
Wannan mumunanr hatsarin ya faru ne a ranar Talata, 6 ga watan Fabrairu a babban titin Legas zuwa Ibadan kuma mutane hudu sun riga mu gidan gaskiya.
3) Hatsarin tankan dakon man fetur na gadar Ojuelegba
Hatsarin ya afku ne a ranar Talata, 19 ga watan Yuni gadar Ojuelegba, mutum biyu sun rasu a dalilin hatsarin.
4) Hatsarin tankar dakon man fetur na Suleja
Mutane hudu ne suka riga mu gidan gaskiya sakamakon wannan hatsarin da ya faru a ranar Juma'a, 29 ga watan Yuni, a garin Suleja dake jihar Neja.
5) Hatsarin gadar Otedola dake Legas
Wannan shine hatsari mafi muni a cikin jerin hadduran kuma ya faru ne ranar Alhamis, 28 ga watan Yuni a gadar Otedola dake unguwar Alausa a jihar Legas, mutane 12 sun rasu kuma a kalla motocci 40 sun kone.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng