Saura kwana 1 ta gama bautar kasa wani dan sanda ya tura ta kiyama

Saura kwana 1 ta gama bautar kasa wani dan sanda ya tura ta kiyama

Wata yar bautar kasa mai shekaru 23 ta rasa ranta a sanadiyyar harbi da wani dan sanda yayi

Saura kwana 1 ta gama bautar kasa wani dan sanda ya harbeta har lahira
Saura kwana 1 ta gama bautar kasa wani dan sanda ya harbeta har lahira

Wata yar bautar kasa mai shekaru 23 ta rasa ranta a sanadiyyar harbi da wani dan sanda yayi.

Marigayiyar mai suna Linda Angela Igwetu ta rasa ranta ne a rabar Laraba da misalin karfe 3 na safe wanda ya rage saura kwana daya a yaye su daga bautar kasar da suke wanda ake gudanarwa a yau Alhamis.

Yar uwar marigayiyar mai suna Chiyenya Igwetu ta bayyana afkuwar haka a shafinta na Twitter "@chinny3bs".

DUBA WANNAN: Atiku ya bukaci 'yan majalisa dasu kara taso da maganar 'yan sandan jiha

"Miss Linda Igwetu wadda zata kammala Bautar kasar ta a yau Alhamis dinnan wadda aka turata gwaji a kamfanin Outsource Global Company dake Mabushi a babban birnin tarayya".

"Ta kammala aikin ta na ranar da misalin 11 na dare inda ta tsaya tare da wasu abokanan ta akan shirye shiryen da zasu gudanar a wajen yayesu.

"Sun bar gida da misalin 3 na dare, anyi harbin ne a daidai Ceddi plaza wanda wani jami'in dan sanda mai suna Benjamin Peter yayi, inda harsashin ya sami Linda wanda a take ta fara zubda jini" ta bayyana a shafin nata na twitter.

Anyi kokarin kaita asibitin Garki saidai daga baya aka bayyana rasuwar ta.

Yayin da manema labarai ke ganawa da mai magana da yawun yan sandan birnin tarayyar DSP Anjuguri Manzah yace sun tabbatar da afkuwar lamarin. Inda yace "muna ci gaba da bincike a kan lamarin.

Yan sandan dake bakin aiki a lokacin da abun ya faru sunce suna kokari ne su ceci wadda ta rasa ranta wanda a tunanin su anyi garkuwa da ita ne.

"Sunyi kokarin tsaida abun hawan amma basu dakata ba a kokarin su na tsaida motar ne suka harbi tayar motar saboda suna tunanin masu garkuwa da mutane ne amma harbin ya kuskure ya sami Linda."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng