Zubar da mutunci: Yadda wasu malamai 5 suka dirkawa dalibar wata makarantar sakandire ciki a Kebbi ciki
An kori malamai 5dake koyarwa a makarantar sakandiren kwalejin kimiyya dake Birnin Kebbi saboda yiwa wata dalibar aji shida (SS3) ciki.
Kazalika, hukumar makarantar ta kori yarinyar.
Majiyar jaridar PM News ta rawaito cewar, an kori dalibar da malaman bisa shawarar kwamitin bincike da makarantar ta kafa, kuma ya mika sakamakon bincikensa da shawarwari ga hukumar makarantar ranar Litinin.
A cewar kwamitin, “lokacin da muka titsiye dukkan malaman, sun tabbatar da cewar suna aikata lalata da dalibar, saboda haka muka shawarci hukumar makarantar ta sallame su daga aiki.”
Malaman da aka kora sun mika takardun neman afuwa ga hukumar makarantar.
Shugaban makarantar, Malam Muhammed Mahuta, ya shaidawa jaridar PM News cewar lokacin da abun ya faru bay a makarantar, yana asibiti inda ya yi zaman jinya. Saidai mataimakinsa, Malam Oumar Woulandakoye, dake rikon kwaryar shugabancin makarantar lokacin da abin ya faru, ya tabbatar da faruwar lamarin.
DUBA WANNAN: Kwarya ta bi kwarya: Kurma ya auri Berbiya, hotunan biki
“Mun kori malaman gabadayansu, amma sun rubuto takardar neman afuwa tare da basu dama ta karshe. Mun shawarce su da su jira abinda hukumar kwalejin kimiyya zasu yi a kan lamarin domin sun fara zama domin tattauna batun,” a cewar Malam Oumar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng