Ajali ba ya wuce ranarsa: Wani mutum ya kashe matarsa akan Naira 200

Ajali ba ya wuce ranarsa: Wani mutum ya kashe matarsa akan Naira 200

- Saurin fushi ya kai wani ango ya baro shi

- Bayan da yayi ta lakadawa matarsa duka har lahira

- Yanzu haka ya shiga hannu ido ya rana fata

Bisa laifin dukan matarsa da yayi akan Naira 200 wanda ya yi sanadin barinta duniya, wata kotun Majistiri ta tisa keyar Henry Anaele zuwa gidan kaso har tsawon kwanaki 30, kafin daga bisani a dawo domin sauraren shari'ar.

Ajali ba ya wuce ranarsa: Wani mutum ya kashe matarsa akan Naira 200
Ajali ba ya wuce ranarsa: Wani mutum ya kashe matarsa akan Naira 200

Mista O. O Olatunji wanda ne alkalin kotun, ya ce za a cigaba da tsaron wanda ya aikata laifin a gidan kaso na Ikoyi dake jihar Legas ba tare da bada belinsa ba.

KU KARANTA: Wani dan kuka ya kashe Uwarsa har lahira, hukuncin da ya biyo baya yayi dai-dai

Anaele dan shekaru 40 da haihuwa ya roki gafarar kotu, amma hakan bai samu ba saboda ana tuhumarsa da laifin kisa.

Jami'in dan sandan da ya gabatar da karar a gaban alkali Sufeto Adams, ya ce wansa ake tuhumar ya aikata laifin ne a ranar 15 ga watan da ya gabata da misalin karfe 11:45 na dare, saboda zargin matarsa da yayi bisa wani dalilin satar layi.

Adams ya ce "wani ne ya bawa matarsa kyautar kudi Naira 200, wanda hakan shi bai kwanta masa a raiba, don hakan ne yasa ya shiga dukan matar tasa wanda a dalilin haka tace ga garinku nan".

Laifin ya saɓawa kundin manyan laifuka na jihar Legas karkashin sashi na 223 na shekarar 2015.

Kotun ta ɗage zaman har sai 6 ga watan Agustan shekarar nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng