Ci da buguzum: An kama su yayin da suke tsaka da yiwa jama’a fashi da bindigar bogi
Hukumar ‘yan sanda reshen jihar Ogun tayi nasarar cafke wasu ‘yan fashi biyu dake amfani da bindigar roba domin razana jama’a kafin su kwace masu abun hannunsu.
An kama ‘yan fashin biyu; Michael Iheanacho na kasuwar kasa da kasa ta Alaba dake jihar Legas da Jamiu Haruna na titin Kembiri a Legas, yayin da suke tsaka da yiwa jama’a fashi a rukunin gidajen Idaniyi ranar 2 ga watan Yuli.
Kakakin ‘yan sanda a jihar, Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa manema labarai cewar wasu mazauna unguwar ta Idaniyi ne suka kira ofishin ‘yan sanda na Agabara yayin da ‘yan fashin suka shiga gidan wani mutum, Ugochukwu Umeh tare da yunkurin kwace motarsa kirar Honda mai lamabar mallaka GBE 717 GH.
DUBA WANNAN: A karon farko, Mikel Obi ya yi magana a kan tsaro a Najeriya bayan sace mahaifinsa
Oyeyemi ya kara da cewa, bayan samun kiran wayar ne sai suka tura jami’ansu inda suka yi nasarar kama biyu daga ‘yan fashin uku, tare da taimakon yan bijilanti.
Kazalika, kwamishinan ‘yan sanda a jihar, Ahmed Iliyasu, ya bayar da umarni a mayar da ‘yan fashin biyu da aka kama ya zuwa sashen binciken fashi da makami na rundunar ‘yan sanda atre da bayyana cewar yanzu haka ya baza jami’ai domin farautar daya dan fashin day a tsere.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng