'Yan sanda sun kama shugaban 'yan fashin da yaransa suka dakatar dashi a Kano
Hukumar Yan sanda reshen jihar Kano ta sanar da kama wani shugaban kungiyar fashi da makami mai suna Sulaiman Mujahid wanda suka dade suna adabar mazaunan Sheka qauters a Kano.
Wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami'an hulda da jama'a na yan sandan jihar, SP Magaji Musa Majia ya ce an kama shugaban yan fashin ne a watan Yuni.
Sanarwan ta ce, "A ranar Talata 19 ga watan Yunin 2018 misalin karfe 12.30 na safe wani gawuratcen shugaban yan fashi Mujahid Suleiman dake zaune a Sheka Quaters ya jagoranci mambobin kungiyarsa: Rabiu Sama'ila da Uwardawa Abo da wani Al-Amir zuwa fashi amma duk an kama su," inji sanarwan.
KU KARANTA: Kwastam ta kama motocci 11 makare da shinkafar kasashen waje
Sanarwan ta cigaba da cewa yan fashin sun shiga gidaje uku dauke da adduna da wukake inda suka yiwa mutane da yawa duka tare da ji wa wasu daga cikinsu rauni kafin suka yi musu fashin kayayakinsu.
'Yan fashin da ake zargi sun gudu da wata mota kirar Toyota Vibe, sun kuma sace kudade da wasu abubuwa masu daraja wanda kudinsu ya kai N3.9 miliyan.
Shugaban kuniyar, Mujahid ya amsa laifin aikata fashin kuma ya ambaci wani Abdul-aziz a matsayin wanda ya bashi bayanan sirri kafin akan gidajen uku kafin ya tafi yi musu fashi.
Kwamishinan ya kuma ce jami'an yan sanda suna aiki ba dare-ba-rana don ganin an kamo sauran mambobin kungiyar yan fashin.
Kazalika, ya kara da cewa hukumar ba zata amince da duk wasu masu kokarin tayar da zaune tsaye ba musamman wannan lokacin da zabe ke karatowa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng