Faransa da Najeriya sun rattaba hannu kan wasu muhimman yarjejeniya biyu
A yau ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin takwaransa na kasar Faransa a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.
Macron ya iso Najeriya da misalign karfe 3:10 na ranar yau, Talata, kuma kai tsaye ya wuce fadar shugaba Buhari bayan ministan Abuja, Mohammed Abuja, da na harkokin kasaashen waje, Geoffrey Onyeama, sun tare shi a filin saukar jirage na Nnamdi Azikiwe dake Abuja.
Bayan wata ganawar sirri tsakanin shugabannin biyu, sun rattaba hannu kan wasu yarjejeniya guda biyu; ta farko ita ce ta bunkasa harkar sufuri da gwamnatin Legas ta kirkira kuma kasar Faransa zata dauki nauyi. Ministar kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun, da Mista Remy Rioux, shugaban wani kamfanin kasar Faransa, Agence Francaise de Development, suka saka hannu a kan yarjejeniyar.
DUBA WANNAN: Kotu ta bayar da umarnin a tsare tsohon minista Muhammed Wakil bayan EFCC ta gurfanar da shi
Kazalika kasashen biyu sun sake kulla wata yarjejeniya a kan tsaftace muhalli da gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun, da Rachel Kolbe, manajan wani kamfani, In Vivo, suka sakawa hannu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng