Shugaban kasar Faransa ya iso Najeriya
Shgaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya iso Najeriya, kamar yadda kafafen yada labarai suka bayyana a jiya cewar shugaban zai kawo wata ziyarar aiki Najeriya.
Jirgin dake dauke da shugaba Macron ya dira a filin tashi da saukar jirage na Nnamdi Azikiwe dake birnin tarayya, Abuja, da misalin karfe 3;10 na ranar yau, Talata, 3 ga watan Yuli.
Ministan harkokin kasashen waje, Geofrey Onyeama, da takwaransa na Abuja, Muhammed Bello,ne suka tarbi Macron a filin jirgin sama na Abuja.
DUBA WANNAN: Dattijo da matashi: Shugaba Buhari ya gana da matashin shugaban kasar Faransa, duba hotuna
Onyeama ya bayyana cewar, "yayin ziyarar sa a Najeriya, Macron zai mayar da hankali ne a kan tattalin arziki da tsaro."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng