Ruwa yayi gyara: Ruwan sama ya rusa gidaje fiye da 100 a Daura
Labari ya zo mana ba da dadewa ba cewa Mutanen Garin Daura inda nan ne Mahaifar Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun ga ta kan su bayan da ruwan sama yayi barna kwanan nan.
Wata mahaukaciyar tsawa ce dai ta yi sanadiyyar rushewar gidaje fiye da 100 a cikin Garin na Daura da ke cikin Jihar Katsina a daren Ranar Lahadi. Manema labarai watau NAN sun ce tsawar ta kuma yi sanadiyyar mutuwar wani Bawan Allah.
A Ranar Lahadin da ta wuce an yi ruwa mai karfi a cikin Garin na Katsina kamar yadda Hukumar bada agaji ta tabbatar. Tun kimanin karfe 3:00 na yamma aka fara ruwan sama wanda har aka kai cikin dare ana zuba shi ba kakkautawa kamar da bakin kwarya.
KU KARANTA: Kasashe 3 da su ka fi ko ina rashin yawan al’umma a Duniya
Abubakar Mashi wani Darekta a Jihar yayi magana a madadin Shugaban Karamar Hukumar Daura inda ya tabbatar da aukuwar wannan ibtila’i. Yanzu dai Gwamnatin Jihar da kuma sauran Hukuma da ‘Yan Majalisu na kokarin agazawa wadanda musibar ta shafa.
Nasiru Yahaya wanda shi ne ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Yankin a Majalisar dokokin Jihar yayi alkawarin daukar nauyin wadanda su ka samu rauni a hadarin. Kwanaki dai wata iska ta rusa gidaje a cikin Katsina inda har Shugaban kasa Buhaari ya kai masu ziyara.
Idan ba ku manta ba, a baya kun ji cewa Majalisar Wakilan Tarayya ta koka da wahalar wutan lantarkin da ake fama da shi a Yankin Garin ba Daura a Jihar Katsina bayan da wata na’urar da ke bada wuta ta buga.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng