Nigerian news All categories All tags
An samu gawar mutane 10 rataye a wani gida, ana binciken musababbin mutuwar su

An samu gawar mutane 10 rataye a wani gida, ana binciken musababbin mutuwar su

A wani yanayi mai daure kai, an samu gawar mutane 11 rataye a wani gida dake birnin Delhi ta kasar Indiya.

Daga cikin mutane 11 akwai yara 2, sannan an samu gawar wata tsohuwa mai shekaru 77 kwance a kasa. Yawancin gawarwakin, an rufe masu fuska sannan an daure masu hannayensu a bayansu.

‘yan sanda sun bayyana cewar sun fara bincike domin gano musabbabin mutuwar mutanen duk da sun samu wata takarda a gidan da aka samu gawarwakin dake nuna cewar al’amarin ya faru ne ta hanyar gudanar da wasu al’adu masa nasaba da bauta.

An samu gawar mutane 10 rataye a wani gida, ana binciken musababbin mutuwar su

Wasu Indiyawa

Mutanen dake zaune a unguwar da lamarin ya faru sun shiga cikin fargaba da zaman dar-dar. Mazauna gidan sun shafe fiye da shekaru 20 suna zaune a birni Delhi tun bayan zuwansu daga garin Rajasthan dake arewa maso yammacin kasar Indiya kuma suna gudanar da sana’o’insu ne a shagon dake kasan gidan, mai bene hawa uku.

DUBA WANNAN: Dattijo da matashi: Shugaba Buhari ya gana da shugaban kasar Faransa, kalli hotuna

Wani dake makwabtaka da gidan, Gurcharan Singh, ne ya fara ganin gawarwakin bayan ya je shagon gidan domin yin sayayya amma kofofin gidan a bude kuma babu kowa a shagon, kamar yadda BBC ta rawaito.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel