Mai horas da 'yan wasan Super Eagles zai ajiye aikin sa

Mai horas da 'yan wasan Super Eagles zai ajiye aikin sa

Rahotanni sun nuna cewa mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya Gernot Rohr yana dab da ajiye aikin sa, inda zai koma kasar Aljeriya domin cigaba da horar da 'yan wasan kasar

Mai horas da 'yan wasan Super Eagles zai ajiye aikin sa

Mai horas da 'yan wasan Super Eagles zai ajiye aikin sa

Rahotanni sun nuna cewa mai horas da 'yan wasan kwallon kafa na Najeriya Gernot Rohr yana dab da ajiye aikin sa, inda zai koma kasar Aljeriya domin cigaba da horar da 'yan wasan kasar.

Kwanan nan kasar Aljeriya ta kori mai horas da 'yan wasan nata, Rabah Madjer bayan ya kasa tabuka komai a kasar, inda kasar ta dinga faduwa wasannin data ke yi da wasu kasashe na sada zumunta, kamar irin su Iran, Saudi Arabia, Cape Verde da kuma kasar Portugal.

DUBA WANNAN: Duba abinda wasu suka ji a jikin su kafin tankar mai ta fashe a Legas

A gabannin tafiya gasar cin kofin duniya ne dai, Gernot Rohr ya tsawaita kwantiraginsa da Najeriya zuwa shekarar 2020, inda daga baya kuma yake cewa babu tabbas cewa aikin nasa zai dore ganin irin rashin nasarar da kungiyar Super Eagles a kasar Rasha.

Kocin wanda ya jima yana aikin horas da 'yan wasan yankin Afrika irinsu Nijar, Burkinafaso da kuma kasar Gabon, ya nuna cewa zai iya tafiyar da tawagar kasar Aljeriya ganin cewar ya horar da kungiyoyi kamar irinsu Bordeaux OGC da kuma Nantes ta kasar Faransa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel