Buhari dalibina ne, ni na kawo shi siyasa - Bafarawa ya kaddamar da takarar shugabancin kasa a PDP

Buhari dalibina ne, ni na kawo shi siyasa - Bafarawa ya kaddamar da takarar shugabancin kasa a PDP

Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, ya kaddamar da takarar sa ta neman jam'iyyar PDP ta tsayar da shi takara shugaban kasa a zaben 2019.

Da yake ganawa da manema labarai jim kadan bayan kammala kaddamar da takarar ta shi a gidansa dake garin Sokoto, Bafarawa ya yi ikirarin cewar shine ya kawo Buhari cikin siyasa.

"Ni kwararren dan siyasa ne. Na samu lokaci mai tsawo ina gwagwarmayar siyasa," a cewar Bafarawa.

Buhari dalibina ne, ni na kawo shi siyasa - Bafarawa ya kaddamar da takarar shugabancin kasa a PDP
Attahiru Bafarawa
Asali: Depositphotos

Sannan ya cigaba da cewa, "Buhari dalibina ne domin nine na kawo shi siyasa. Nine na fara bashi tikitin tsayawa takarar shugabancin kasa lokacin da ya fara tsayawa takara a tsohuwar jam'iyyar ANPP. A saboda haka na san yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati da jam'iyya."

Da yake shagube ga shugaba Buhari shagube, Bafarawa ya bayyana cewar babbar matsalar Najeriya ita ce dora mutanen da basu da gogewa a siyasa su shuganci kasa.

A cewar sa, hakan ne ya saka shugabannin basa biyayya ga manufofin jam'iyya.

DUBA WANNAN: 2019: Jerin tsofin janar-janar na soji dake kulle-kullen kayar da Buhari zabe

Kazalika ya bayyana cewar 'yan Najeriya na bukatar a yiwa tsarin gwamnati garambawul saboda saboda yadda gwamnatin APC ke gudanar da mulkin kasa.

Bafarawa ya kara da cewa ya jinkirta batun kaddamar da takarar sa ne, duk da kiraye-kiraye jama'a, saboda halin da ake ciki a kasar.

Daga karshe ya bukaci magoya bayansa dasu hada kai wuri guda tare da shaida masu cewar ya fito takara ne saboda son da yake yiwa mutanen Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng