Chakwakiyar aure: Idan mijina ya doke ni, ramawa nake yi – Jarumar fim da mijinta ya sabawa kamanni
Wata jarumar shirin fina-finan kudancin Najeriya, Bose Omotoyossi, ta bayyana cewar aurenta da mijinta, dan was an kwallon kafa, Razaq, ya lalace.
Jim kadan bayan sun yi murnar cika shekaru 10 da aure, Bose ta bayyana cewar, mijinta na yawan dukanta hart a kai gab a zata iya jurewa ba, ita ma ta fara ramawa.
Saidai a wata hira da tayi da ‘yan jarida, Bose ta lashe amanta tare da bayyana cewar aurenta da mijinta na nan daram.
“Na gane cewar nayi kuskuren bayyana halin da aurenmu ke ciki a dandalin sada zumunta. Mijina bai taba cewa komai a kan sabanin da muke samu ba a dandalin sada zumunta.
DUBA WANNAN: Hannun matashi, Saminu, da ‘yan sanda suka yiwa dukan tsiya ya fara rubewa, kalli hotuna
“Ranar da muka yi murnar cika shekaru 10 aure ne muka samu wani sabani da ta kai har mijina ya fasa min waya tare da yi min duka, hakan ya bani haushi sosai, domin har yaran mu na kwashe na bar gidansa domin ya fahimci cewar nayi fushi sosai,” a cewar Bose.
Sannan ta kara da cewa, “muna yawan samun sabani da mijina, amma yanzu muna tare kuma muna ziyartar kwararru domin neman shawarwari da taimako a kan yadda zamu zauna lafiya da juna."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng