An raba wa wadanda harin jihar Pilato ya shafa da iyalansu diyya

An raba wa wadanda harin jihar Pilato ya shafa da iyalansu diyya

A jiya ne Gwamnatin jahar Nassarawa tayi ta bada gudunmawar kudi naira miliyan 10 ga wadanda akayi wa barna a jahar Plateau an kai harin ne a ranar Asabar inda akayi wa mutane 200 barna a wasu yankuna na Barikin Ladi dake jihar ta Plateau

An raba wa wadanda harin jihar Pilato ya shafa da iyalansu diyya
An raba wa wadanda harin jihar Pilato ya shafa da iyalansu diyya

Gwamna Umaru Tanko Almakura wanda ya kai ziyarar Jaje tare da sarakunan gargajiya a gidan gwamnatin Jahar Platue sun bayyana hakan akan Wani abu da baza'a lamunta ba.

An raba wa wadanda harin jihar Pilato ya shafa da iyalansu diyya
An raba wa wadanda harin jihar Pilato ya shafa da iyalansu diyya

Munsan cewa wannan abu Wani nauyi ne daya rataya a wuyan jahar ta Plateau gaba daya, a matsayin mu na makotan wannan Jahar ya zama wajibi a garemu mu bada tamu gudunmawar komai kankantar ta kuwa.

Gwamna Lalong ya mika godiyar sa ga jahar Nassarawa inda yake cewa "a kowace jaha akwai mutane na kwarai da kuma akashin haka wadanda suke bada gudunmawa wajen kashe rayuka, duk wadanda suke aikata hakan suke tunanin sun tsira to basu tsiraba a wajen ubangiji, da sannu allah zai toni asirinsu."

DUBA WANNAN: Ta kashe mijinta kan batun kishiya

Gwamnan ya Kara da cewa wadannan da suke tunanin sunfi karfin doka to basu fi ba ya kara da cewa " na fadawa mutanen Platue su kara hakuri su bamu hadin kai da sannu zamu bayyana wadanda sukayi wannan ta'asar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel