'Yan Najeriya dake Haure sun goyi bayan kudirin Atiku na neman kujerar Shugaban Kasa

'Yan Najeriya dake Haure sun goyi bayan kudirin Atiku na neman kujerar Shugaban Kasa

Wata kungiyar 'yan Najeriya dake birnin Dallas a jihar Texas ta kasar Amurka, sun bayyana goyon bayan su kan kudirin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar, na neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Kungiyar ta daura damarar goyon bayan tsohon shugaban kasar ne sakamakon yakinin ta na cewar Atiku yana da duk wata cancanta ta jagorantar kasar nan.

Hakazalika kungiyar ta yanke wannan shawara ne sakamakon kudirin tsohon shugaban kasar na baiwa al'ummar Najeriya dama ta kada kuri'un su a yayin zabe ko ina suke a fadin duniya.

'Yan Najeriya dake Haure sun goyi bayan kudirin Atiku na neman kujerar Shugaban Kasa
'Yan Najeriya dake Haure sun goyi bayan kudirin Atiku na neman kujerar Shugaban Kasa

Shugaban wannan kungiya, Sir Chris Onyeador, shine ya bayyana hakan da cewar za su goyi bayan tsohon mataimakin shugaban kasar ne da yakinin zai rattaba hannu kan dokar da za ta tabbatar da 'yancin su na jefa kuri'un su a lokutan zaben muddin ya zamto shugaban kasa.

DUBA WANNAN: Kotu ta wanke tsohon shugaban hukumar Sojin sama tatas daga laifin Zamba

Bugu da kari kamar yadda shugaban kungiyar ya kuma bayyana, tsohon mataimakin shugaban kasar yana da kudirin sauya fasalin kasar Najeriya cikin watanni shida kacal da zarar ya karbi kargar mulki.

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya ruwaito, kungiyar tana da yakinin Atiku zai inganta harkokin ilimi, wutar lantarki da kuma harkokin noma da za su kawo ci gaba a kasar nan sakamakon wayewar sa gami da hangen nesa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel