Shugaban 'yan daban Sakkwato ya shiga hannun hukuma

Shugaban 'yan daban Sakkwato ya shiga hannun hukuma

Hukumar Yan sanda reshen jihar Sakkwato da sanar da kama wani da ake zargin shine shugaban 'yan daba na Sakkwato wanda aka ce yana da hannu cikin aikata laifufuka da dama cikin shekaru hudu da suka wuce a jihar.

Kakakin hukumar, DSP Cordelia Nwawe ne ta bayyana hakan yayin da take yiwa manema labarai jawabi kan kama shugaban yan daban da wasu mutane 25 a ranar Juma'a a Sakkwato.

KU KARANTA: Tambuwal ya yi magana a kan alakanta shi da kashe-kashen jihar Filato

Ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar 21 ga watan Yuni kuma a yanzu an same shi da hannu cikin laifuka guda takwas.

Shugaban 'yan daban Sakkwato ya shiga hannun hukuma
Shugaban 'yan daban Sakkwato ya shiga hannun hukuma

Nwawe ta ce laifukan sun hada da fashi da makami, cin zalin mutane, makirci don aikata laifuka tare da kasancewarsa mamba haramtatun kungiyoyi da suka kware wajen aikata laifuka.

Nwawe ta kuma kare da cewa wanda ake zargin shine ya kafa kungiyar ta'addanci da akafi sani da Samisa ko Falluja a Hubbare da ke jihar Sakkwato.

Ta kuma bayyana cewa yana da mambobi guda 17 wanda suke zuwa sassa daban-daban na jihar don musguwana wa al'umma.

Har ila yau, Nwawe ta ce hukumar ta kuma damke wasu dilalan miyagun kwayoyi dauke da kwayar da ake zargin ganyen wiwi ne a garin Tamaje na jihar Sakkwato.

Yan sandan kuma sun kama Mayesedine guda 347 da kwalaben haramtacen maganin tare mai dauke da codeine da masu miyagun kwayoyin a yayin wata simame da jami'an hukumar suka kai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel