Kotu ta wanke wani jigo a APC daga zargin karkatar da makuden miliyoyi

Kotu ta wanke wani jigo a APC daga zargin karkatar da makuden miliyoyi

Kotu ta wanke shugaban a jam'iyyar APC na yankin kudancin Ondo, Dr. Taiwo Malumi daga zargin da aka masa na damfara na makuden kudi N40 miliyan.

An dai zargi Malumi ne da damfarar wani Nick Shaiyen, manajan kamfanin Whitehall Management Limited bayan ya sayar masa da gida mai lamba B9, Funtai Court, 3, Ruxton Street, Ikoyi Legas kuma ya tabbatar masa babu wani matsala tattare da gidan.

Ayodele Ignatius Salami, Lauya mai kare Malumi ya roki kotun tayi watsi da karar da aka shigar kan Malumi inda ya bayyana cewa matsalar kasuwanci ne kamar yadda mutanen biyu saka rattaba hannu a kan yarjejeniya a ranar 10 ga watan Nuwanban 2016.

Kotu ta wanke wani jigo a APC daga zargin karkatar da makuden miliyoyi
Kotu ta wanke wani jigo a APC daga zargin karkatar da makuden miliyoyi

KU KARANTA: Zamu dawwama a talauci muddin bamu rage haihuwa barkatai ba - Ministan Buhari

A yayin da yake yanke hukunci, Justice Saliu Saidu ya ce bisa hujojin da bangarorin biyu suka gabatar, dukkansu sun amince za su tafi wajen yan sanda domin suyi sulhu tunda dama abinda ake so kenan.

Alkalin ya kara da cewa dukkan takardun da aka gabatar gaban kotun bai nuna wata alama na cewa Malumi ya yi niyyar damfarar wanda ya shigar da karar ba.

"Bisa ka'idar yarjejeniyar da kuka amince dashi, wannan lamarin harka ce tsakanin yan kasuwa saboda haka baka da ikon zuwa kotu ka canja zancen. Ka riga ka amince da yarjejeniyar tun farko," inji Alkalin.

"Dukkan bangarorin biyu za suyi biyaya ga yarjejeniyar da suka kulla, Saboda haka na sawake wa mai shigar da kara da wanda aka kawo kararsa, nayi watsi dukkan tuhumar da akeyi a wannan shari'ar."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164