NDLEA ta kama dilolin kwaya guda 60, da kwayoyi masu yawan gaske

NDLEA ta kama dilolin kwaya guda 60, da kwayoyi masu yawan gaske

A ranar juma'ar nan ne hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen jihar Kogi tace ta kama mutane 60 masu safarar miyagun kwayoyi da kuma kwayoyi masu nauyin kilogram 976.2, a tsakanin watan Afirilu da watan Yuni

NDLEA ta kama dilolin kwaya guda 60, da kwayoyi masu yawan gaske
NDLEA ta kama dilolin kwaya guda 60, da kwayoyi masu yawan gaske

A ranar juma'ar nan ne hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA), reshen jihar Kogi tace ta kama mutane 60 masu safarar miyagun kwayoyi da kuma kwayoyi masu nauyin kilogram 976.2, a tsakanin watan Afirilu da watan Yuni.

DUBA WANNAN: Abubuwan da referee ya fadawa Mikel Obi jiya bayan an tashi wasa

Alhaji Idris Bello, kwamandan hukumar ta jihar Kogi, ya bayyana hakan a wata tataunawa da yayi da manema labarai a Lokoja.

Bello yace masu safarar miyagun kwayoyin sun hada da maza 56 da mata 4.

"Hukumar ta kwace kilogram 976.2 na miyagun kwayoyi da suka hada da hodar ibilis mai nauyin 974.5 a kankanin lokaci "yace.

Kamar yanda ya fada, cikin su, mutane 4 an yanke musu hukuncin zama a gidan yari. Ya kara da cewa 28 daga cikin su an sake su, sai 28 daga cikin su suna tare dasu.

Bello yace ranar yaki da shan miyagun kwayoyi da safarar su ta duniya, ta shekarar 2018 da akayi a 26 ga watan Yuni, anyi ne don wayar ma da mutane kai akan hatsarurrukan dake tattare da miyagun kwayoyi.

Bello yace sama da kashi 60 na laifukan ta'addanci a duniya ana danganta su ne da illar miyagun kwayoyi.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng