Majalisa ta amince da naddin sabon mataimakin gwamnan jihar Bauchi
A yau Juma'a ne majalisar Jihar Bauchi a tantance kana ta amince da Audu Katagum a matsayin sabon mataimakin gwamnan Jihar.
Majalisar ta amince da mataimakin gwamnan ne a zaman da tayi karkashin jagorancin kakakin majalisar Kawuwa Damina.
Majalisar ba ta bata lokacin wajen tantancewar ba don basu dauki sama da mintuna biyar ba wajen tantance Katagum.
KU KARANTA: Zargin rashawa: Gwamnatin tarayya ta sake gurfanar da wani Sanata a kotu
Dan majalisa mai wakiltan yankin Bura, Abdullahi Abdulkadir ya bukaci a amince da Katagum saboda dama ya yi aiki a matsayin shugaban ma'aikata a karkashin gwamnatin gwamna Mohammed Abubakar.
Ibrahim Katagum, dan majalisa mai wakiltan Katagum ne ya goyi bayan bukatar tantance shi cikin gagawa.
Daga bisani majalisar ta tabbatar dashi a matsayin mataimakin gwamnan jihar Bauchi.
A baya, Legit.ng ta kawo muku rahoto inda tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Injiniya Nuhu Gidado ya yi murabus daga mukaminsa a ranar 24 ga watan Mayu.
Gwamnan kuma a watan Yuni ya zabi shugaban ma'aikatansa, Katagum don maye gurbin Gidado da ya yi murabus a matsayin mataimakin gwamnan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng