Shugaba Buhari ya saka hannu kan wasu sabbin dokoki biyu

Shugaba Buhari ya saka hannu kan wasu sabbin dokoki biyu

A jiya Alhamis 28 ga watan Yuni ne shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wasu sabbin dokoki biyu kamar yadda Sanata Ita Enang ya bayyana.

A lokacin da ya ke jawabi ga manema labarai a gidan gwamnati, Enang ya ce dokokin sune Dokar Koyar makamashin aiki na likitoci na shekarar 2018 da kuma Dokar biyan la'ada ga garuruwan da ke samar da wutan lantarki na shekarar 2018.

Buhari ya saka hannu kan wasu sabbin dokoki biyu

Buhari ya saka hannu kan wasu sabbin dokoki biyu

A cewar Enang, dokar koyar da makamashin aikin zai fayyace yadda za'a rika horas da likitoci da kuma likitocin hakora a Najeriya. Kwallegin karatun gaba da digirin farko na Najeriya ne za ta rika kula da shirin.

KU KARANTA: Zamu dawwama a talauci muddin bamu rage haihuwa barkatai ba - Ministan Buhari

Ya ce an bullo da shirin ne don mutanen da suka kammala karatun digiri na farko a likitanci da tiyaya ko liktocin hakora (MB. Bsc, MB. CH, B, BDS) ko makamacinsu kuma wanda suka kammala hidiman kasa wato NYSC.

"Anyi dokar ne saboda a tsaftace harkan samar da lafiya a Najeriya ta hanyar bayar da horaswa ingantace.

"Hakan zai sa mutane daga kasashen ketare su kara amincewa da fannin samar da lafiya na Najeriya har ma su rika tururuwa zuwa kasar don neman magani," inji shi.

Ita kuma dokar wutan lantarkin za ta bawa ministan lantarki da makamashi ikon bayar da umurni da kara wa hukumar kula da lantarki na kasa (NERC) ikon zartar da hukunce-hukunce.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel