A karon farko bayan tsige Super Eagles, Ahmed Musa ya aiko sakon sa ga 'yan Najeriya
Tauraron kungiyar kwallon kafa ta Najeriya (Super Eagles), Ahmed Musa, ya aiko da sakon gaisuwa da godiya ga masoyan sa bisa goyon baya da suka nuna masa da kungiyar Super Eagles a wasannin da suka buga a gasar cin kofin duniya a kasar Rasha.
An cire Najeriya daga gasar cin kofin a ranar Talata bayan kasar Argentina ta doke ta da ci 2 - 1.
Musa ya bayyana cewar, duk da yaji matukar ciwo da takaicin cirewar da aka yiwa Najeriya, ya ce dole ya jinjinawa masoya Super Eagles bisa sadaukar wa da goyon bayan da suka nuna.
Musa bai gama warwarewa da raunin da ya samu ba lokacin da Najeriya ta fafata da kasar ta Argentina.
Masoya Super Eagles sun kafe kan cewar alkalin wasa ya yi masu magudi, ta hanyar hana su bugun daga kai sai mai tsaron gida bayan dan wasan kasar Argentina ya taba kwallo da hannu a cikin da'irar mai tsaron kasa.
Saidai hukumar kula da wasanni ta duniya, wato FIFA, ta kare alkalin wasan tare da bayyana cewar sabuwar dokar bayar da bugun daga kai sai mai tsaron gida da aka yi ce ta saka alkalin wasan yin hakan.
DUBA WANNAN: Tsagwaron Kishin kasa: Zuciyar wani kwararren likitan Najeriya ta buga saboda cin da aka yiwa Najeriya jiya a Rasha
Ko a jiya saida jaridu suka wallafa wani labari da tsohon fitaccen dan wasan kasar Kwadebuwa, Didier Drogba, ke cewar alkalin wasa ne ya cuci Najeriya a wasan domin tabbas dan wasan baya na kasar Argentina ya taba kwallo da hannu amma aka hana Najeriya bugun daga kai sai mai tsaron gida.
Ba wai iya Drogba keda wannan fahimta ba a kan wasan na Najeriya da kasar Argentina. Shi ma kaftin din kungiyar Super Eagles, John Mikel Obi, ya kafe kan cewar hana Najeriya bugun daga sai mai tsaron gidan, rashin adalci ne.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng