Laftanar Janar Buratai ya kaddamar da madatsar ruwa da Sojoji suka gina a Yobe

Laftanar Janar Buratai ya kaddamar da madatsar ruwa da Sojoji suka gina a Yobe

Babban hafsan Sojan kasa, Laftanar Janar Tukur Yusuf Buratai ya kaddamar da wani sabon madatsar ruwa a karamar hukumar Fika na jihar Yobe a kokarinsa na taimaka ma jama’an garin da ruwan sha, tare da inganta alaka tsakanin Sojoji da fararen hula.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Buratai, wanda ya samu wakilcin babban hafsan rundunar Soji rukuni na uku, Manjo Janar Benhamin Ahanotu ya kaddamar da madatsar ruwan ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuni a garin Fika.

KU KARANTA: Taskar Kannywood: Yan kallo sun gaji da ganin Jamila Nagudu, Washa, Gabon, Tsamiya – Inji Darakta

A jawabinsa, Buratai yace: “Mun yi wannan aiki ne don sauke nauyin da ya rataya akanmu na ganin mun taimaka ma jama’an wannan yanki da ruwan sha da sauran amfani, haka zalika wannan aiki zai kara kyautata alaka tsakaninmu da al’ummar wannan yanki.

“Ina fata wannan aiki zai kara hada kan mu gaba daya, saboda shi ruwa bai san addini ko kabila ba, dukkaninmu muna bukatarsa don cigaba da rayuwa, ba tare da la’akari da addininmu ko kabilarmu ba.” Inji shi.

Shi kuwa Sarkin Fika, Muhammad Abali yaba ma rundunar Sojan kasa ya yi, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito, inda yace: “Hakan ruwa a wannan yanki na da matukar wahala, saboda irin yanayin kasar, don haka jama’anmu na matsalar ruwa sosai.

“Amma wannan aiki da kuka yi zai rage wahalar ruwa, don haka muna mika cikakken godiyarmu ga rundunar Sojin kasa, musamman ga babban hafsan Sojan kasa saboda da ya bada umarni ayi wannan aiki a Fika.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng