Rikicin makiyaya da manoma: Obasanjo ya kai ziyarar jajantawa garin Jos

Rikicin makiyaya da manoma: Obasanjo ya kai ziyarar jajantawa garin Jos

Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya yi kira ga gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari da ta tabbatar da cikakken binciken kwakwaf don gano masu hannu cikin kisan kiyashi da aka yi ma jama’a a jihar Filato, inji rahoton gidan talabijin na Channels.

Obasanjo ya yi wannan kira ne a ranar Laraba, 27 ga watan Yuni yayin wata ziyarar jaje da ya kai jihar, inda ya samu ganawa da gwamnan jihar, Simon Lalong, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

KU KARANTA: Tsohuwar Ministan Jonathan ta mayar da naira miliyan 640 cikin lalitar gwamnati

A cewar Obasanjo, kamata ya yi a gano musabbabin dake haddasa rikicin, don shawo kansa tare da kare kara faruwar hakan a gaba; “Mu gano gaskiyan abinda ke janyo wannan rikici, dole ne akwai abinda ke haddasawa.

“Idan har bamu yi haka ba, tabbas za’a cigaba da zubar da jinni babu gaira babu dalili, don haka ya zama wajibi mu magance musabbabin wadannan rikita rikita, saboda mun sani duk wata matsala tana da hanyar maganceta.” Inji shi.

Obasanjo ya kara da cewa a yayin da ake gudanar da wannan bincike, ya dace gwamnatin tarayya ta hada kai da gwamnatin jihar Filato da kananan hukumomin da abin ya shafa, har ma da shuwagabannin al’ummomin yankin.

Dayake nasa jawabin, gwamna Simon Lalong ya bayyan rikicin a matsayin abin takaici, inda yace zaman lafiya fi zama dan Sarki, don kuwa idan akwai zaman lafiya a jihar Filato, tabbas duk dan kirki zai ji dadi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel