Kotu ta hana bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame

Kotu ta hana bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, babbar Kotun tarayya dake zamanta cikin yankin Gudu a babban birnin kasar nan na Abuja, ta yi watsi da buƙatar daurarren tsohon gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame, da ya nemi ta bayar da belin sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon gwamnan na ci gaba da zaman bai wa diga-digan sa hutu na tsawon shekaru 14 a gidan kaso na Kuje dake garin Abuja, bisa aikata laifin almundahana ta dukiyar al'umma a yayin da yake cin ganiyyar sa kan kujerar mulki.

Mai shari'a Adebukola Banjoko, wanda a ranar 30 ga watan Mayun da ta gabata ya zartar da hukuncin zama gidan kaso kan tsohon gwamnan na jihar Taraba sakamakon hannun sa cikin karkatar da akalar Naira Biliyan 1 na dukiyar jihar sa, ya kuma soke bukatar sa ta beli a ranar Larabar da ta gabata da cewar ba ta da madogara.

Kotu ta hana bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame
Kotu ta hana bayar da belin tsohon Gwamnan jihar Taraba, Jolly Nyame

Alkalin ya yi watsi da wannan bukatar ne inda ya bayyana cewa, beli yana cacanta ga wanda aka zartar da hukuncin sa bisa wasu muhimman dalilai da suka hadar har da rashin lafiya.

DUBA WANNAN: Joe, mahaifin fitaccen Mawaki Michael Jackson ya riga mu gidan gaskiya

Rahotanni sun bayyana cewa, tsohon gwamna Nyame ya nemi kotun ta bayar da belin sa ne domin ya samu damar ci gaba da kulawa da lafiyar sa da ya saba amfani da magungunan gargajiya sakamakon cutar Hawan Jini da ciwon sukari da yake fama da su.

Sai dai Alkali Banjoko ya jaddada cewa, babu wasu gamsassun dalilai ko hujjoji dake tabbatar da bukatar Nyame na cancantar samun beli.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, wani Matashi mai shekaru 35 ya shiga hannu da laifin zakkewa wata karamar yarinya 'yar shekara 5 a jihar Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng