Joe, mahaifin fitaccen Mawaki Michael Jackson ya riga mu gidan gaskiya

Joe, mahaifin fitaccen Mawaki Michael Jackson ya riga mu gidan gaskiya

Joseph Walter Jackson, Mahaifin fitaccen marigayin mawakin nan, Michael Jackson, ya riga mu gidan gaskiya kamar yadda kafofin watsa labarai daban-daban na duniya suka bayyana wannan mummunan rahoto a ranar yau ta Laraba.

Joseph Jackson dai ya bar duniya a gidan sa na birnin Los Angeles dake Kasar Amurka yana mai shekaru 89 bayan ya sha fama da cutar Daji ta Saifa.

Legit.ng ta fahimci cewa, mutuwa ta cimma Joseph ne bayan kwanaki biyu da cikar shekaru tara da mutuwar dan sa, Michael da bar duniya a ranar 25 ga watan Yunin 2009.

Joseph ya haifi 'ya'ya 11 a yayin rayuwar sa tare da matarsa Katherine Jackson da aura tun a shekarar 1949.

Tarihi ya bayyana cewa, an haifi Joseph ne a ranar 26 ga watan Yulin 1928 a yankin Fountain Hills dake garin Arkansas a kasar Amurka.

DUBA WANNAN: Aikin Hanyar Kano zuwa Abuja zai samar da Ayyuka sama da 3000 - Minista

Ko shakka babu duniya ta yadda cewa Iyalin Joseph na daya daga cikin shahararrun dangi a fadin duniya sakamakon zakakuran yara da haifa musamman Michael da kanwar sa Janet da har gobe suka yiwa duniyar waka wankin babban bargo.

Bugu da kari dalilai da bincike sun tabbatar da cewa, ba bu wani ma'abocin nishadantar da al'umma da ya shiga gaban Marigayi Michael yayin rayuwar sa har kawowa yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng