Nigerian news All categories All tags
An kama mutane 3 da suke da hannu a rikicin Filato

An kama mutane 3 da suke da hannu a rikicin Filato

A ranar Larabar nan ne wasu dakarun rundunar soja na musamman wadanda ake yi musu taken "Operation Save Haven", suka kama wasu mutane uku wadanda suke da hannu a kashe - kashen da ake yi a jihar Filato a yanzu

An kama mutane 3 da suke da hannu a rikicin Filato

An kama mutane 3 da suke da hannu a rikicin Filato

A ranar Larabar nan ne wasu dakarun rundunar soja na musamman wadanda ake yi musu taken "Operation Save Haven", suka kama wasu mutane uku wadanda suke da hannu a kashe - kashen da ake yi a jihar Filato a yanzu.

Mun samu rahoton dakarun sun samu nasara kama wadanda ake zargin a kauyen Gashish dake karamar hukumar Barkin Ladi dake jihar Filaton.

DUBA WANNAN: An gano wani sahihin maganin Cancer

An gurfanar da wadanda ake zargin a garin Jos babban birnin jihar Filato, tare da wasu mutane 14, wadanda suma aka kama su da hannu a ta'asar da ake yi yanzu a jihar.

Majiyar mu Legit.ng ta samu rahoton cewar rikicin ya shafi kauyuka 11 wadanda suke a karamar hukumar Barkin Ladi, inda aka yi asarar rayuka da dukiya ta biliyoyin nairori.

A lokacin da ake gabatar da masu laifin, mai magana da yawun rundunar sojin Manjo Umar Adams, ya sanarwa da manema labarai cewar sun kama masu laifin ne a lokacin da suke gyaran bindigogin su.

Adam yace mutane biyu a cikin su Fulani ne sai kuma wani mutum daya dan kabilar Birom, wadanda a yanzu haka suke rigima da junan su akan wurin kiwo.

"Duk mun san da cewar kwanakin baya, an kaiwa wasu kauyuka hari a karamar hukumar Barikin Ladi, mun kama wadannan mutane ukun da hannu akan wannan hare - hare da aka kai yankunan.

"Mun samu nasarar kama su a dai - dai lokacin da mutanen mu suke rangadi a yankin wuraren da abin ya faru, inda muka kama su da bindigogi 8.

"Sannan kuma sauran mutane 14 mun kama su da tada zaune tsaye a fadin jihar nan."

Adam yace har yanzu suna gabatar da bincike akan wadanda ake zargin, sannan kuma ya bada tabbacin zasu cigaba da kokari wurin kawo karshen tashe - tashen hankula a jihar dama kasa baki daya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel