Rashin tausayi: Boko Haram sunyi wa mutane 7 yankan rago a kan neman itace

Rashin tausayi: Boko Haram sunyi wa mutane 7 yankan rago a kan neman itace

- 'Yan kungiyar Boko Haram sun hallaka mutane bakwai a dajin kauyen Damboa

- Mutanen sun shiga dajin don saro itace da za su sayar ne yayin da suka hadu da yan ta'addan

- Yan ta'addan sun yanka mutune bakwai yayin da wasu daga ciki suka tsira da raunuka

A kalla mutane bakwai ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka tsira da munanan raunuka bayan sunyi gamu da mayakan kungiyar Boko Haram a kauyen Damboa da ke Borno a jiya Talata.

Assha: Boko Haram sunyi wa wasu mutane 7 yankan rago yayin da suka shiga daji neman itace
Assha: Boko Haram sunyi wa wasu mutane 7 yankan rago yayin da suka shiga daji neman itace

Kamar yadda 'yan banga suka bayyana, lamarin ya afku ne a garin Damboa yayin da mazauna kauyen shiga daji neman itace amma mayakan Boko Haram din su kayi musu yankan rago.

KU KARANTA: EFCC ta nemi a dauke shari'ar Shekarau daga kotun Kano saboda dalilan tsaro

Guda bakwai daga cikinsu sun mutu sai dai wasu daga cikinsu sun tsira da raunukan harsashi kamar yadda Sahara reporters ta ruwaito.

"Wannan ranar bakin ciki ne a garin Damboa. Wasu mutane sun shiga daji neman itace da za su sayar amma sai suka hadu da yan kungiyar Boko Haram kuma su kayi musu yankan rago," inji dan bangan.

"Mutane bakwai sun mutu wasu daga cikin mutanen kuma sun tsira da raunuka a jikinsu bayan sun dawo Damboa da rana."

A wata labarin Legit.ng ta ruwaito cewa wasu gungun yan bindiga dadi sun kashe dakarun rundunar Sojin kasa guda biyu a wani harin kwantan bauna da yan bindigar suka kai musu a cikin karamar hukumar Guma, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun shirya wani tarko ne a daidai lokacin da Sojojin ke sintiri a a tsakanin kauyukan Umenger da Bakin korta, duk a cikin mazabar Mbadewem, a inda Sojoji biyu suka mutu, wasu kuma suka jikkata

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel