Atiku ya yi rabon miliyoyin nairori ga mutanen da ibtila’i ya fada musu a jihar Bauchi

Atiku ya yi rabon miliyoyin nairori ga mutanen da ibtila’i ya fada musu a jihar Bauchi

Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya kai ziyarar jajantawa ga al’ummar jihar Bauchi inda ya bayyana alhininsa game da bala’in ruwa da iska mai karfi ya fada mawa a jihar, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga jajen da Atiku yayi musu a fadar Sarkin Bauchi, Rilwanu Adamu, bugu da kari ya basu kyautar kudi naira miliyan goma don rage musu radadin asarar da suka tafka.

KU KARANTA: Inna Lillahi wa Inna Ilaihi rajiun: Kananan Yara 500 sun mutu a Zamfara

Atiku ya yi rabon miliyoyin nairori ga mutanen da ibtila’i ya fada musu a jihar Bauchi
Atiku

Atiku yayi addu’ar Allah ya jikan wadanda suka rigamu gidan gaskiya, sa’annan yayi fatan Allah ya mayar ma wadanda suka yi asarar dukiya da mafi alheri; “Na zo da naira miliyan 10 don saukaka ma wadanda abin ya shafa, da fatan Alllah ya kare faruwar haka a gaba.” Inji shi.

Dayake nasa jawabin, Sarkin Bauchi ya bayyana Atiku Abubakar a matsayin cikakken masoyin jihar Bauchi na hakika, “Muna matukar da godiya da wannan taimako da ka baiwa mutanen jihar Bauchi, wannan ya nuna kai masoyinsu ne.” Inji Sarki.

Atiku ya yi rabon miliyoyin nairori ga mutanen da ibtila’i ya fada musu a jihar Bauchi
Atiku

Daga karshe Atiku ya garzaya garin Azare na jihar Bauchi don jajanta ma yan kasuwar garin da suka tafka asara sakamakon wutar gobara da ta yi barna a babbar kasuwar garin, inda ta kona sama da shaguna dubu daya kurmus.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng