An kama masu garkuwa da mutane 12 a Sokoto
Hukumar tsaro ta Civil Defence, reshen Sokoto, ta tabbatar da kama wasu mutane 12 dake garkuwa da mutane a kananan hukumomi 4 dake jihar.
Kwamandan hukumar na jihar, Mista Babangida Dutsinma, ya sanar da hakan a jiya, Talata, yayin wata ganawa da ya yi da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN).
A cewar Dutsinma, an kama masu garkuwa da mutanen ne bayan sun aike da wasikar barazanar sace wasu masu arziki 6 dake karamar hukumar Tureta muddin ba a biya su kudi, miliyan N12m ba.
DUBA WANNAN: Kotun koli ta sahalewa Trump hana musulmi daga jerin kasashen nan shiga kasar Amurka
Ya kara da cewar, kafin hukumar su ta samu labarin abinda yak e faruwa tuni mutanen har sun biya masu garkuwar miliyan N2m ta hannun mai isar masu da sako.
Dutsinma ya bayyana cewar sun yi nasarar kwato makamai daga hannun ‘yan ta’addar da suka hada da bindigu da sauran su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng