Gwamnatin Jihar Gombe ta bayar da tallafin N10m da Kayan agaji ga wadanda bala'in Bauchi ya shafa
Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Ibrahim Hassan Dankwambo, ya bayar da tallafin kayan agaji da kuma Naira miliyan 10 ga mutanen da bala'in guguwa da ruwan sama ya shafa a jihar Bauchi kwanaki kadan da suka gabata.
Kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya bayyana, Gwamna Dankwambo ya gabatar da kayan agajin ne tare da miliyoyin Dukiya ga gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar a ranar Talatar da ta gabata.
Cikin jawaban sa gwamnan ya bayyana cewa, sun ziyarci jihar Bauchi ne da tawagar sa domin jajanta wa gwamnati da al'ummar dangane da afkuwar ibtila'in da salwantar da rayuka gami da asarar dukiya.
Dankwabo ya kara da cewa, akwai kyakkyawar alaka da dangantaka tsakanin jihar Bauchi da Gombe, inda ya ce duk lamarin da ya shafe ta ya shafi jihar sa ne.
Rahotanni sun bayyana cewa, gwamnan ya bayar da agajin mota guda ta buhunan shinkifa da kuma wata ta buhunan Masara baya ga Naira Miliyan goma na tallafi.
KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta cafke wata Mata da laifin cin zarafi a Garin Abuja
Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon Mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar, ya ziyarci jihar ta Bauchi domin jajanta wa tare da bayar da tallafin naira miliyan goma ga wadanda lamarin shafa.
Hakazalika jaridar ta ruwaito cewa, a makon da ya gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar ta Bauchi domin jajanta wa al'ummar da gwamnatin ta dangane da afkuwa wannan tsautsayi da ba ya wuce ranar sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng