Jerin 'yan wasan Najeriya da za su taka leda a karawar da za a yi da Argentina
Najeriya ta fitar da sunayen yan wasan da za su taka leda a wasar da za'a buga da kasar Argentina a gasar cin kofin duniya.
Zakaran dan wasan Najeriya, Ahmed Musa da ya jefa kwallaye biyu a ragar Iceland shima yana cikin jerin wanda za su buga a yau din inda Kelechi Iheanacho da Victor Moses za su kasance suna kai hari tare dashi.
Sai dai dan wasan kungiyar Arsenal Alex Iwobi har yanzu yana zaune a benchi.
Ga dai jerin sunayen yan wasan
23. Uzoho
6. Balagun
5. Ekong
22. Omeruo
2. Idowu
11. Moses
4. Ndidi
10. Mikel
8. Etebo
7. Musa
14. Iheanacho
Najeriya wadda itace kasa mai yan wasan mafi karancin shekaru a gasar za ta kara da Argentina wanda suke da shararen dan kwallon duniya Lionel Messi.
A lokacin da suka kara a shekarar 1994, dan wasa mai dabara Claudio Cannigia ne ya jefa kwallo na biyu inda aka tashi wasan 2 - 1 sai dai hakan bai hana Najeriya zuwa zagaye na gaba ba.
A wasan da suka buga a baya, Messi ya jefa kwallaye biyu a raga inda shima Ahmed Musa ya jefa kwallaye biyu. Super Eagles din suna kokarin duk yadda za suyi don doke Argentina a karo na farko a gasar cin kofin duniya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng