Kungiyar kare hakkin bil’adama ta bayyana su waye ke kashe mutane a Najeriya da sunan makiyaya
- Kungiyar kare hakkin bil’adama (NHRC) ta bayyana cewar ba makiyaya ba ne ke kasha mutane a jihohin Benuwe da Filato ba
- Wasu ‘yan bindiga sun hallaka mutane a kalla 120 a jihar Filato a ranar Asabar, 23 ga watan Yuni, da ta gabata
- Shugaban NHRC, Tony Ojukwu, ya bayyana cewar ba za a rasa hannun Boko Haram a kashe-kashen ba
Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa (NHRC), Tony Ojukwu, ya bayyana cewar a zargi kungiyar Boko Haram, ba makiyaya ba, a kashe-kashen da suka ki-ci-suka-ki cinyewa a jihohin Benuwe da Filato.
Ojukwu ya bayyana cewar gwamnatin Najeriya bata son bayyana cewar kuniyar Boko Haram c eke kai hare-haren saboda yin hakan zai zama tamkar karyata ikirarin tan a cewar ta murkushe kungiyar.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari ya bayyana masu hannu a kasha-kashen jihar Filato, ya fadi abinda suke son cimma
Ojukwu na wadannan kalamai ne a jiya, Litinin, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a ofishin sa dake Abuja, domin bayyana dalilin da ya sa hukumar bata har yanzu ba ta yi wani kokari na kawo karshen kashe-kashen ba.
Ojukwu ya bayyana cewar, mayakan Boko Haram sun koma kai hare-hare yankin arewa ta tsakiya ne saboda matsin lamaba da suke fuskanta daga dakarun soji a yankin arewa maso gabas.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng