Ciyamomi 23 sun karbi rantsuwar kama aiki daga hannun gwamna El-Rufai a Kaduna (Hotuna)

Ciyamomi 23 sun karbi rantsuwar kama aiki daga hannun gwamna El-Rufai a Kaduna (Hotuna)

Gwamnan jihat Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufai ya rantsar da sabbin shuwagabannin kananan hukumomi ashirin da uku da suka samu nasara a zabukan kananan hukumomi da suka gudana a kwanakin baya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

A yayin bikin rantsarwar da ya gudana a ofishin sakatren gwamnatin jihar, El-Rufai ya shawarci Ciyamomin dasu kasance masu gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da adalci a mulkinsu.

KU KARANTA: Gasar cin kofin Duniya: Magen sa’a ta bayyana Najeriya za ta samu nasara akan Ajantina

“Ku kiyayi nuna son kai, domin haka ya saba ma rantsuwar da kuka dauka na yin adalci, Allah ya zabeku ne a matsayin shuwagabanni a kananan hukumominku ba tare da ya duba addini, ko kabilarku ba, don haka ya zama wajibi ku yi adalci.” Inji shi.

Gwamnan ya bayyana ma sabbin ciyamomin cewa majalisar dokokin jihar ta samar ma sahihan dokoki da suka baiwa shugaban karamar hukuma wuka da nama a sha’anin mulki, “Nan bada jimawa ba ma’aikatan kananan hukumomi zata shirya muku bita don bayyana muku abinda da sabon dokar kananan hukumomi ya kunsa.” Inji shi

Sai dai a wani hannun kuma, akwai shari’un da aka shigar dangane da sakamakon zabe na kananan hukumomi guda uku, da suka hada da Chikun, Kajuru da Jaba, yayin da ba’a yi zabe a karamar hukumar Kaura ba, wannan ya sa gwamna ya nada shugaban riko.

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel