Kalli hotuna: Kwankwaso ya ziyarci Fayose a Ekiti, ya yiwa dan takarar PDP kamfen
- Toshon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai ci, Rabi’u musa Kwankwaso ya ziyarci gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose
- Rahotanni sun bayyana cewar ya yiwa dan takarar gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP kamfen
- Kwankwaso ya gana da Atiku a ranar da jam’iyyar APC ke taron zaben sabbiin shugabanni a karshen makon day a gabata
A jiya, Litinin, ne jigo a jam’iyyar APC kuma tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ziyarci gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose.
Jaridar The Nation ta rawaito cewar Kwankwaso ya bayyana cewar ya kai ziyara jihar ta Ekiti ne domin yin kira ga kowanne bangare a kan muhimmancin yin zaben gwamnan jihar cikin lumana, saidai kakakin Fayose, Lere Olayinka, ya sanar da manema labarai cewar Kwankwaso ya yiwa dan takarar jam’iyyar PDP, Farfesa Kolapo Olusola, yakin neman zabe.
Ana rade-radin cewar nan bada dadewa ba Kwankwaso zai koma jam’iyyar PDP bayan an kasa sasanta rikicin siyasar dake tsakanin sad a gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje.
DUBA WANNAN: Babu wanda zai iya daure ni saboda na kiyaye mutunci na – Shugaba buhari ya cikawa ‘yan adawa baki
An jiyo Kwankwaso na fadin cewar, “duka da zabe ba yaki ba ne amma dole a bawa jama’a abinda suka zaba kuma suke so.”
Fayose, a jawabin sa, ya jinjinawa Kwankwaso bisa ziyarar day a kai masa.
Kwankwaso na daga cikin jihga-jigan ‘ya’yan APC da basu halarci taron zaben sabbin shugabannin jam’iyyar da aka yi a karshen makon day a gabata ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng