Yadda na ketare tarkon wani lakcara dake son lalata da ni – Dalibar jami’ar Bayero

Yadda na ketare tarkon wani lakcara dake son lalata da ni – Dalibar jami’ar Bayero

Wani shiri da gidan Radiyon BBC ke gabatarwa da ake kira “Adikon zamani’ ya kai ziyara jami’ar Bayero dake Kano domin jin ta bakin dalibai, musamman mata, a kan zargin tilasta masu yin lalata da wasu balagurbin malamai ke yi.

Shirin ya kai wannan ziyara ne biyo bayan wata dambaruwa da ta faru tsakanin wani Farfesa a jam’iar Obafemi Awolowo dake jihar Osun da wata daliba.

A hirar da aka yi da wasu daliban jami’ar Bayero, sun shaidawa wakiliyar BBC cewar su ma su na fama da matsalolin neman su da lalata da wasu batagari daga cikin malaman ke yi.

Yadda na ketare tarkon wani lakcara dake son lalata da ni – Dalibar jami’ar Bayero

Jami’ar Bayero, Kano.

Wata dalibar jam’iar ta bayyana cewar daya daga cikin malaman ta ya nuna yana son ta amma koda ta shaida masa cewar ita ba soyayya ta kawo ta jami’a ba sai ya yi mata barazanar cewar shi ma akwai ranar sa domin zata yi kwas din sa. Dalibar t ace barazanar malamin ta saka ta kin daukar kwas din sa domin gudun kada ya huce haushin sa a makin jarrabawar ta.

DUBA WANNAN: An kama malamin addini da laifin kisan wata karuwa domin yin tsatsiba, duba hotuna

Kazalika wani dalibin makarantar ya bayyana yadda ya fada tsaka mai wuya a hannun wani lakcara saboda kawai yana son wata yarinya da shi ma Lakcaran ke so.

Dakta shamsudden Umar na sashen kula da walwalar dalibai (Student Affairs Division) yak are jami’ar tare da bayyana cewar, kada daliban su ji shayin kai rahoton duk malamin day a neme su da lalata domin, a cewar sa, jami’ar Bayero na daga cikin jami’o’in da basa wasa wajen daukan mataki a kan irin wadannan balagurbin malamai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel