Da dumi-dumi: Shugaban taron jam’iyyar APC ya matsa layar zana yayin da ake jiran ya sanar da sakamakon zaben da aka kammala

Da dumi-dumi: Shugaban taron jam’iyyar APC ya matsa layar zana yayin da ake jiran ya sanar da sakamakon zaben da aka kammala

A yayin da aka kamalla kada kuri’un kujeru 8 a zaben shugabannin APC da aka fara jiya, an nemi shugaban taron, gwamna Badaru Abubakar na jigawa, an rasa a yayin da ake jiran sa domin sanar da sakamakon zaben.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo sun bar wurin taron bayan isar su da misalign karfe 10:20 na safe.

A yayin da ake zaman dakon sakamakon kujerun da aka kuri’un zaben ‘yan takarar su, jirgin sama mai saukar ungulu na hukumar ‘yan sandan Najeriya ya fara shawagi a sararin samaniyar filin taron, Eagle Square.

Da dumi-dumi: Shugaban taron jam’iyyar APC ya matsa layar zana yayin da ake jiran ya sanar da sakamakon zaben da aka kammala

Shugaba Buhari ya kada kuri'ar sa a wurin taron jam'iyyar APC

Daliget da suka kada kuri’a na cigaba da sulalewa daga wurin. Ana has ashen cewar, Daliget na barin wurin ne saboda gajiya da suka yi da zama, tun jiya.

DUBA WANNAN: Tirka-tirka: Buhari, Tinubu da gwamnoni sun rabawa daliget mabanbantan sunayen ‘yan takarar da zasu zaba

Magoya bayan gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha, da na sakataren gudanarwa mai barin gado na jam’iiyar APC na cigaba da kawo rudani a wurin taron duk da jami’an tsaro na kokarin ganin ba a samu barkewar rikici a tsakanin sub a kamar yadda ta faru a jiya ba.

Ya zuwa yanzu, da muka kamala wannan rahoto, babu tabbacin lokacin da za a sanar da sakamakon zaben saboda ba a san inda shugaban taron da mambobin sa suka shiga ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel