Boko Haram: Wani sabon hari ya salwantar da rayukan Mutane 4 da raunata 6 a garin Konduga

Boko Haram: Wani sabon hari ya salwantar da rayukan Mutane 4 da raunata 6 a garin Konduga

Mutane hudu ne suka rasa rayukan su yayin da shida suka raunata sakamakon wani sabon hari na Boko Haram da ya afku a ranar Juma'ar da ta gabata cikin kauyen Tunkushe dake karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Harin ya afku ne yayin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam cikin al'ummar mazauna wannan kauyen da suke bacci a wani budadden wuri kamar yadda kamfanin dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito.

Boko Haram: Wani sabon hari ya salwantar da rayukan Mutane 4 da raunata 6 a garin Konduga
Boko Haram: Wani sabon hari ya salwantar da rayukan Mutane 4 da raunata 6 a garin Konduga

Bukar Dalorima, wani mazaunin wannan yanki da ya tabbatar da afkuwar harin ya shaidawa manema labarai cewa, bayan fashewar bam din 'yan ta'adda sun kuma bude wuta ta harsashin bindiga kan mai uwa wabi.

Legit.ng ta fahimci cewa, a sanadiyar haka ne wasu daga cikin mazauna yankin su ka rasa rayukan su yayin da wasu suka raunata kamar yadda Dalorima ya bayyana.

KARANTA KUMA: Makiyaya sun salwantar da Rayukan Mutane 18 a wani Kauyen Jihar Adamawa

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, Edet Okon, ya bayar da tabbacin sa na dangane da wannan lamari da ya bayyana cewa ya afku ne da misalin karfe 1.00 na daren ranar Juma'ar da ta gabata a kauyen Tunkushi dake Konduga.

Okon ya kara da cewa, hukumar ta tanadi karin jami'ai a yankin domin tsananta tsaro yayin da tuni an ci gaba da gudanar da harkoki a yankin kamar yadda aka saba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng