Tsofin gwamnoni uku a arewa da EFCC ba ta taba bincikar su ba

Tsofin gwamnoni uku a arewa da EFCC ba ta taba bincikar su ba

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ne ya kafa hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) a shekarar 2004 domin bincike tare da hukunta masu yiwa tattalin arzikin kasa ta'annati da zagon kasa.

Tun bayan kafa hukumar ta EFCC binciken ta ya fi karfi a kan tsofin gwamnoni, kuma binciken tsofin gwamnonin ya fi daukar hankalin 'yan Najeriya.

Binciken tsohon gwamna ba bakon abu ba ne a Najeriya. Tsofin gwamnoni da yawa sun gurfana gaban kotu bayan kammala zangon mulkin su bisa zargin su da almundahana ko karkatar da dukiyar gwamnati ba.

Wasu gwamnonin jihohin arewa da suka taba kammala mulki ba tare da hukmar EFCC ta bincike su ko gurfanar da su sun hada da;

1. Bukar Abba Ibrahim

Ya mulki jihar Yobe daga shekarar 1999 zuwa 2003 amma abun mamaki hukumar EFCC bata taba lissafa shi cikin tsofin gwamnoni da take bincike ba.

Tsofin gwamnoni uku a arewa da EFCC ba ta taba bincikar su ba

Sanata Bukar Abba Ibrahim

DUBA WANNAN: Abubuwa 4 da za su iya hana PDP tsayar da Sule Lamido

2. Marigayi Umar Musa Yar'adua

Matawallen Katsina kuma tsohon shugaban kasa, Umar Musa, ya zama gwamna a jihar Katsina a karo na farko a shekarar 1999 kafin daga bisani a sake zaben sa a karo na biyu a shekarar 2003.

Ya samu shaidar tsantseni da kyamar barna, babu mamaki don bai taba fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC ba.

Tsofin gwamnoni uku a arewa da EFCC ba ta taba bincikar su ba

Tsofin gwamnoni uku a arewa da EFCC ba ta taba bincikar su ba

3. Adamu Aliero

Tsohon gwamnan jihar Kebbi daga shekarar 1999 zuwa 2007, Aliero ya yi nasarar kammala zango biyu a gwamnati ba tare da hukumar EFCC ta gurfanar da shi ba.

Tsofin gwamnoni uku a arewa da EFCC ba ta taba bincikar su ba

Adamu Aliero

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel