An kai ga musayar naushi tsakanin jama'ar APC a gaban Baba Buhari

An kai ga musayar naushi tsakanin jama'ar APC a gaban Baba Buhari

Wasu daliget sunyi musayar naushi a taron kasa na jam'iyyar APC da ke gudana a Eagles Square Abuja yayin da shugaba Muhammadu Buhari ke karanto jawabinsa.

Rikcin ya kaure ne bayan wasu magoya bayan gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo sun iso rumfar da aka ware don deleget din jihar Imo.

Da isowarsu sai suka umurci magoya bayan mataimakin jihar gwamna Imo, Eze Madumere su tashi su bar wajen.

KU KARANTA: Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

An kai ga musayar naushi tsakanin jama'ar APC a gaban Baba Buhari
An kai ga musayar naushi tsakanin jama'ar APC a gaban Baba Buhari

Kin tashi daga rumfar ne ya janyo wani daga cikin masu tsaron gwamna Okorocha na musamman wanda ake kira "Okorocha Good Governance" ya kaiwa magoya bayan Madumere duka kuma wajen ta kacame.

Anyi fatali da shugaban kungiyar masu adawa da Rochas Okorocha, Hillary Eze tare da sauran magoya bayansa da wasu zabubun shugabanin jami'iyyar na jihar.

Shima Osita Izunazo, sakataren shirye-shiryen na jam'iyyar APC na Imo wanda shima yana adawa da Okorocha ya bar rumfar ba shiri.

Hakazalika, bangarori biyu na jam'iyyar APC daga jihar Delta suma sunyi irin wannan rikicin a rumfar tasu.

Wakilan jam'iyyar da suke rikicin sunyi ta jifan juna da tsintsiya wadda itace alamar jam'iyyar.

A baya, shugaba Muhammadu Buhari ya ce jam'iyyar za'a kara samun hadin kai bayan taron jam'iyyar. Ya kuma yi kira ga duk wadanda suke da ganin anyi musu ba dai-dai ba suyi hakuri.

Ciyaman din jam'iyyar mai barin gado John Odigie Oyegun ya mika godiyarsa da shugabanin jam'iyyar bisa gudunmawar da suka bashi.

Sai dai bai ambaci Bola Tinubu ba da tsohon ciyaman din jam'iyyar Tony Mommoh cikin wadanda ya yiwa godiya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel