Matsaloli 5 da jam'iyyar APC ya kammata ta warware kafin gangamin taron ta

Matsaloli 5 da jam'iyyar APC ya kammata ta warware kafin gangamin taron ta

A yau ne jam'iyyar APC za ta gudanar da taron ganganminta na shekara-shekara inda ake sa ran za'a zabi sabbin shugabanin jam'iyyar domin fuskantar babban zaben 2019. Sai dai nasarar jam'iyyar ya dogara kan yadda sakamakon taron ya kasance ne musamman yadda ake samun wasu matsaloli tsakanin wasu 'ya'yan jam'iyyar wanda hakan yasa wasu ke barazanar ficewa ba muddin ba'ayi gyara ba.

Ga wasu matsaloli 5 da masu hasashe ke ganin ya kamata jam'iyyar ta warware su kafin gudanar da taron kamar yadda The Cable ta wallafa.

Matsaloli 5 da jam'iyyar APC ya kammata ta warware kafin gangamin taron ta
Matsaloli 5 da jam'iyyar APC ya kammata ta warware kafin gangamin taron ta

1. Rikicin nPDP: Wani babban abinda ke ciwa APC tuwo a kwarya shine korafe-korafen da tsaffin yan PDP da suka dawo APC keyi na zargin wariya da bita da kulli da su kayi ikirarin ana musu a gwamnatin.

Mambobin nPDP sun hada da Bukola Saraki, Yakubu Dogara da Rabiu Musa Kwankwaso da sauransu sun rubuta wasika ga shugaban jam'iyyar John Odigie-Oyegun inda suka lissafa matsalolin da suke fuskanta a jam'iyyar duk da gudun mawar da suka bayar a zaben 2015.

Anyi kokarin yin sulhu a zamansu da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo sai dai daga baya sunyi watsi da taron bayan an janye wasu daga cikin masu tsaron Saraki da Dogara. Sun nemi ganawa da shugaba Buhari sai dai hakan ba ta yiwu ba.

DUBA WANNAN: Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

2. Sakayyar da za'a yiwa 'yan shugabanin jam'iyyar da aka janye karin wa'adin da akayi musu: A ranar 27 ga watan Fabrairu ne APC ta kara wa John Odigie-Oyegun da sauran shugabanin jam'iyyar shekara daya kafin su mika ragamar mulkin ga sabbin shugabani da za'a zaba.

Sai dai bayan wata daya katcal, shugaba Buhari ya nuna rashin amincewarsa da karin wa'adin inda ya ce ya sabawa ka'idojin jam'iyyar. Kafin haka, jagora a jam'iyyar, Bola Ahmed Tinubu ya nuna rashin goyon bayansa ga karin wa'addin.

Hakan yasa dole aka janye karin wa'adin sai dai wasu na ganin idan ba'a yiwa tsaffin shugabanin wata sakayya ba akwai yiwuwar za su iya tada kayan baya nan gaba.

3. Rarabuwar kawunan 'yan jam'iyyar a wasu jihohi: Kafin a samu rarabuwar bangarori a jam'iyyar, akwai wasu jihohi da ake samun sa-in-sa tsakanin manyan jam'iyyar da ke jihar misali jihohin Kaduna, Kano, Kwara, Rivers, Kogi, Imo da Oyo.

Misali a Kaduna, jam'iyyar ta rabu kashi biyu inda wasu ke biyaya ga gwamna Nasir El-Rufai, wasu kuma na tare da Sanata Suleiman Hunkuyi da Shehu Sani. Abubuwa sunyi kamari da aka ce gwamnan jihar ya bayar da umurnin rushe sakatariyar yan bangaren Suleiman Hunkuyi wanda hakan ya janyo sanatocin Kaduna suka hana gwamna izinin karbo bashi daga bankin duniya.

A jihar Kogi kuma Dino Melaye ne ke artabu da gwamna Yahaya Bello yayinda shi kuma gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ke gwabzawa da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

4. Rashin kammaluwar aikin kwamitin sulhu ta Tinubu: Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa kwamitin sulhu karkashin Bola Tinubu don dinke barakar da ke tsakanin 'ya'yan jam'iyyar da basu ga maciji sai dai shi kanshi Tinubu yana bukatar a sulhunta shi da shugaban jam'iyyar John Odigie-Oyegun tun bayar da yaki amincewa da karin wa'addin da akayi masa kuma daga baya ya zargi Oyegun da kawo cikas ga aikin kwamitin nasa.

Sai dai Oyegun ya musanta zargin da Tinubu ya yi masa inda ya ce zai bashi dukkan goyon bayan da ya ke bukata sai dai duk mai lura da abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar ya san na ciki na ciki.

5. Gudanar ta taruka daban-daban tare da tashin hankali yayin tarrukan: An samu rarabuwar kai a sama da jihohi bakwai inda 'ya'yan jam'iyyar suka gudanar da zabuka daban-daban, a wasu jihohin kuma wasu 'yan jam'iyyar sun kauracewa taron.

Uwar jam'iyya kuma ta ce ba za tayi maraba da duk wasu shugabanin jam'iyya da aka zaba a jihohin da aka yi zabe guda biyu saboda rarrabuwar kan 'yan jam'iyyar, ko yaya jam'iyyar za ta warware wannan matsalar cikin lalama?

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel