Sufeto Janar ya yunkura domin kawo karshen Jinkiri cikin Albashin 'Yan sanda
Legit.ng ta fahimci cewa akwai yiwuwar wasu jami'an 'yan sanda su fara gudanar da sallolin dare domin aiwatar da addu'o'i na son barka da alheri ga sufeto Janar na 'yan sanda Ibrahim K. Idris.
Hakan na iya kasancewa a sakamkon yunkurin shugaban hukumar na kawo karshen jinkiri da tsaiko cikin albashin jami'an na 'yan sanda da ya bayyana cewa, ba bu wanda ya ke da wata isa ta rike makogoron albashin jami'an hukumar sa.
Sufeto Janar Idris ya bayyana hakan ne a ranar Juma'ar da ta gabata a shelkwatar hukumar dake garin Abuja yayin binciken takardu na mukaman jami'an tsaro na jihohi 36 dake fadin kasar nan da ya kasance cikin wani ɓangare na ayyuka na cikar sa shekaru biyu rike da hukumar.
Ya tabbatar da cewa, jagororin hukumar sun dukufa wajen gudanar da ayyuka tare da ofishin akawun gwamnatin tarayya domin magance matsaloli da kalubalai wajen biyan jami'an 'yan sanda albashin su.
DUBA WANNAN: Shahararren mai garkuwa da Mutane, Evans, ya yi hayar sabon Lauya
Ya kara da cewa, a yayin da kasar nan take jami'an 'yan sanda fiye da 300, 000 ana fuskantar alubalai wajen biyan su albashi sai dai muddin akwai shinfida ta ingatattun matamai za a magance wannan matsala da haka za ta cimma ruwa.
Ya bayyana jami'an sa cewa, "a duk lokacin da ku ka samu tangarda dangane da albashin ku to ku tabbatar kun bayyana domin kuwa albashi hakkin ku ne kuma ba bu wanda ya cancanci riƙe ma ku albashi."
A yayin haka kuma jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, Shugaban na hukumar 'yan sanda ya kuma ziyarci daliban makarantar kungiyar Matan Aure na jami'an da kuma Asibitin 'yan sanda dake Unguwar Garki a garin na Abuja.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng