Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

Fitaccen marubucin nan na Najeriya , Farfesa Wole Soyinka ya bayyana tsohon Shugaban kasar, Cif Olusegun Obasanjo a matsayin shugaban da yafi kasancewa munafiki a duk tarihin kasar, ya kuma dau alwashin yi masa tonon silili a ranar 3 ga watan Yuli.

Ya yi wannan magana ne a daren Juma'a yayin wata liyafa da aka shirya don murnar zagayowar ranar yan jarida na duniya da aka gudanar a Abuja.

Soyinka yana amsa tambayar da a kayi masa ne game da irin sukar da ya ke yiwa tsohon shugaban mulkin soji Najeriya, marigayi Janar Sani Abacha.

Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka
Ba a taba munafikin shugaban kasa a Najeriya kamar Obasanjo ba - Soyinka

Fitaccen marubucin ya ce ba wai ya karkata zuwa ga shugaba guda bane inda ya kara da cewa yana iya sukar Obasanjo a yau amma ya rungumo shi a gobe.

KU KARANTA: Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

"Ba'a taba yin munafikin shugaban kasa a Najeriya ba kamar Obasanjo," inji Soyinka.

"Obasanjo ya wuce gona da iri... Zan fitar da wata rubutu da zai tona masa asiri a ranar 3 ga watan Yuli a Freedom Park dake Legas.

Duk da cewa Obasanjo da Soyinka duk yan asalin garin Abeokuta ne a Jihar Osun, shugabanin biyu ba sa ga maciji.

Sunyi sulhu a shekarun baya amma sun kuma kula sabuwar gaba bayan Obasanjo ya wallafa litafi a kan tarihin rayuwarsa mai suna 'My Watch'.

A cikin litafin Obasanjo ya fadi wasu kalamai marasa dadi a kan Soyinka inda ya ke ikirarin Soyinka bai san siyasa ba, shi kawai ya fi bajinta ne wajen farauta da dandana barasa.

Hakan yasa Soyinka ya mayar masa da martani inda bayyana tsohon shugaban kasan a matsayin "munafiki da keke-dakeke kuma tantirin makaryaci" wanda bashi da abinda ke faranta masa rai fiye da cin mutuncin mutane.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel