Kabilar Ibo a sun yunkuro kan batun kama Sanatansu da DSS tayi

Kabilar Ibo a sun yunkuro kan batun kama Sanatansu da DSS tayi

Wata babban kungiyar kabilar ibo mai suna 'Igbo Bu Igbo' ta yi Allah-wadai da abinda da ta kira 'cin fuska da barazana da tsare yan siyasar da yan kasuwa na kabilar ibo da wasu jami'an tsaro masu azarbabi keyi'.

A wata sako mai dauke da sa hannun shugaba da kakakin kungiyar, Dr. Law Mefor-Anueyiagu da Jude Ndukwe, kungiyar ta ce bayan kama Sanata Abaribe da a kayi a yau, abin ya fito fili cewa akwai makarkashiyar da ake shiryawa ne wulakantawa da musgunawa Ibo.

Sanarwan da ta cigaba da cewa duk da sun amince babu wanda ya fi karfin doka ta yi aiki a kansa, ba za su saka idanu suna kallo ana cin mutuncin shugabaninsu ba gyra ba dalili ba tare da bin dokar kasa ba.

Kabilar Ibo a sun yunkuro kan batun kama Sanatansu da DSS tayi
Kabilar Ibo a sun yunkuro kan batun kama Sanatansu da DSS tayi

KU KARANTA: Lafiya jari: Illoli 5 da shan ruwan sanyi keyi a jikin dan-adam

Kungiyar tayi kira ga yan Najeriya na gari da masu rajin kare hakkin bil-adam da kasashen waje su dubi irin tsarin da aka dako na yin amfani da hukumomin gwamnati wajen musgunawa mutanen da ke adawa da ra'ayoyin gwamnati.

Sanarwar ta kuma ce Sanata Enyinnaya Abaribe Sanata na a Najeriya kuma idan har ma da gaske akwai wasu tuhume-tuhume da ake masa, abinda ya dace shine a aika masa da gayyata amma ba a kama shi ta hanyar da za'a zubar masa da mutunci ba.

Kungiyar ta ce komin rintsi komin wuya, ba za ta yi watsi da shugabanin ta da gwamnati ke musgunawa ba kamar yadda ba suyi watsi da wanda aka yiwa makamanta irin wannan a baya ba.

Da haka ne kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya ta gagauta sakin Sanata Abaribe domin yana daya daga cikin shugabani da matasan ke koyi da su ba ma a kasar Ibo kadai ba har da sauran bangarorin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164