Babban labari: Abubuwa guda 3 da suka taba sanya Buhari fashewa da kuka
Ba kasafai aka saba ganin manyan mutane suna kuka ba, musamman kuka a bainar jama’a, sai dai ba wai hakan na nufin basa kukan bane, kawai dai abinka da manya, ba’a cika ganin haka bane saboda ya iya zama alamar gajiyawa.
Wannane ya sanya Legit.ng gudanar da binciken kwakwaf don ganin ko shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya taba fashewa da kuka a bainar, wanda kuma binciken namu ya tabbatar da Kukan Buhari. Ga dai wasu lokutta uku da Buhari ya zubar da hawaye.
KU KARANTA: Kashe kashe a Zamfara: Gwamnatin Buhari ta caccaki gwamna Abdul Aziz Yari
A yayin ziyarar da ya kai a ranar Alhamis, 21 ga watan Yuni zuwa babbar kasuwar garin Azare da gobara ya lakume ta a ranar Lahadi, an hangi shugaba Muhammadu Buhari ya zubar da hawaye a yayin da yake jajanta ma yan kasuwar.
Haka zalika wani lokaci da shugaba Buhari ya zubar da hawaye a bainar jama’a shi ne a yayin yakin neman zaben shekarar 2011 sakamakon damuwa da yake ciki sakamakon halin da yan Najeriya ke ciki a wancan lokaci.
Na Uku kuma shine a lokacin yakin neman zaben shekarar 2015, shugaba Buhari ya fashe da kuka sakamakon shaukin da ya dabaibaye shi a lokacin da ya hadu da wata tsohuwa mai kaunarsa a jihar Kebbi, marigayiya Hajia Fadimatu Mai Talle Tara, wanda ta bashi gudunmuwar naira miliyan daya.
Sai dai ya kamata mai karatu ya sani zubar da hawaye ba wai alamar gajiyawa bace, ko wata gazawa ba, illa dabi’a ce kawai ta dan Adam, tunda wasu sukan yi kuka a lokacin farin ciki, wasu kuma a lokacin bakin ciki, yayin da wasu ke yi a duka lokacin biyu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng