Kada ku damu da Kidahumancin nPDP - Adamu ga APC
A ranar Alhamis din da ta gabata ne Tsohon gwamnan gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nemu shugabannin jam'iiyar APC akan su yi watsi da kidahumanci da wauta ta kungiyar nPDP.
Adamu ya bayyana cewa da'awar kungiyar nPDP ta neman martaba da kuma tsayuwar daka domin ganawa da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba wani abu ne face neman yaudara, barazana da yiwa shugaban kasa da jam'iyyar sa zamba cikin aminci.
Tsohon gwamnan wanda kuma ya kasance shugaban kwamitin Majalisar dattawa kan harkokin noma ya bayar da wannan sanarwa sakamakon gabatowar gangamin jam'iyyar ta su ta APC.
Ya yabawa shugaba Buhari dangane da nuna halin ko oho cikin al'amurran nPDP, inda ya danka lamarin su a hannun mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da kuma shugabannin jam'iyya.
Sanata Adamu ya jaddada cewa, lokaci ya yi da ya kamata jam'iyyar ta yi watsi da duk wasu ababe ko wasu mutane masu yunkurin kawar da alkiblar shugaba Buhari da janye hankalin sa wajen ci gaba da gudanar da al'amurran gwamnatin sa.
KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta yiwa jami'an ta 51 ado na ƙarin girma a jihar Katsina
Hakazalika tsohon gwamnan ya yabawa shugaba Buhari dangane da sanya hannu kan kasafin kudin 2018 duk da tangarda da ya fuskanta bayan kusan kwanaki 200 da gabatar da shi a gaban Majalisar dokoki ta tarayya.
Ya kuma yabawa kwamitin tsara gangamin jam'iyyar su tare da fatan alheri a gare shi inda ya nemi dukkanin 'yan takara da wakilai akan hada kai da juna wajen goyon bayan kwamitin domin sauke nauyin da ya rataya a wuyan sa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng