Babban magana: Jaruma Hadiza Gabon ta fusata, tana shirin kwancewa wasu zani a kasuwa

Babban magana: Jaruma Hadiza Gabon ta fusata, tana shirin kwancewa wasu zani a kasuwa

Shahararriyar jarumar nan ta shirya fina-finan Hausa, Hadiza Aliyu Gabon na shirin kwancewa wasu mutane dake rike da kudinta zani a kasuwa.

Bisa ga sakonnin da jarumar ta fitar, tace duk wani mai rike da kudin ta ya shirya fuskantar fushin ta idan baiyi gaggawa biyan bashin da take bin sa ba.

Jarumar ta kai makura kuma kamar yadda ta sanar bata son jin wani labari, kudinta kawai take bukata kuma idan ba'ayi hakan ba zata fallasa sunayen masu.

Babban magana: Jaruma Hadiza Gabon ta fusata, tana shirin kwancewa wasu zani a kasuwa
Babban magana: Jaruma Hadiza Gabon ta fusata, tana shirin kwancewa wasu zani a kasuwa

Gabon tace bata bukatar wadanda take bi bashi su kira ta ko su tura mata sakon. Iya sakon da take son ta gani daga gare su shine alamar an tura mata kudinta.

Cikin kudin ta dake hannun jama'a akwai miliyan N2.8, dubu N350, dubu 75 da kuma dubu N30.

KU KARANTA KUMA: Fusataccen malami ya mari dan karamin yaro saboda ya ki daina kuka a lokacin addu’a

Kamar yadda ta sanar, ciki akwai kudin aikin da tayi ba gama biyanta da kuma kasuwanci da tayi shima ba'a biya ta kudin ta ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku lalube mu a: Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Ko Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko labari, ku tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel