EFCC ta shirya tuggu ga wani tsohon gwamna da ya kwashe kwanaki 30 yana yar buya

EFCC ta shirya tuggu ga wani tsohon gwamna da ya kwashe kwanaki 30 yana yar buya

Bayan kwashe sama da kwanaki Talata yana yar buya da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, daga karshe dai jami’an hukumar sun kure ma wani tsohon gwamna gudu, inda suka isa gidansa a ranar Laraba, 20 ga watan Yuni.

Legit.ng ta ruwaito wannan tsohon gwamnan ba wani bane, face na jihar Kebbi, Usman Saidu Nasamu Dakingari, inda EFCC tace ta sha wahala kafin ta samu mika masa sammacin tuhume tuhumen da take yi masa, sakamakon yar buya da ya shiga yi da ita.

KU KARANTA: Yan kunar bakin wake sun tayar da bama bamai a cikin barikin Sojojin Najeriya

EFCC ta shirya tuggu ga wani tsohon gwamna da ya kwashe kwanaki 30 yana yar buya
Dakingari da takardar Tuhumar

Sai dai yayin da jami’an hukumar suka isa gidansa dake GRA Birnin Kebbi, sun gamu da wani mazaunin gidan mai suna Mohammed Danladi, wanda ya karbi takardar tuhumar, tare da takardar umarnin Kotu da ya basu damar yin hakan.

A shirin EFCC, a ranar Laraba ne ya kamata ta gurfanar da Dakingari a gaban babbar Kotun tarayya dake jihar Kebbi tare da wasu mutane biyu, Sunday Dogonyaro, Abdullahi Yelwa, da Garba Rabiu Kamba kan zarginsu da handame kudi naira miliyan dari bakwai (N700,000,000) da tsohuwar ministan man fetir,Diezani Allison Madueke ta basu.

EFCC ta shirya tuggu ga wani tsohon gwamna da ya kwashe kwanaki 30 yana yar buya
Yayin mika tuhumar

Sai dai hukumar bata samu damar tasa keyarsu gaban Kotu ba sakamakon sun ki amsa gayyatarta, kuma suna buya daga jami’anta, banda Garba Rabiu, wanda ya kai kansa da kansa, da wannan ne Alkalin Kotun Johnson Ojogban ya bada umarnin mika musu takardar tuhumar ta hannun lauyansa, dan gidansu,ko kuma a kai gidan nasu.

A yanzu dai Alkalin y adage sauraron karar zuwa ranar 25 ga watan Yuni, ranar da ake sa ran Dakingari da sauran mutanen biyu zasu gurfana a gaban Kotu don amsa laifukansu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel